Ofishin Jami'an Sanya Ido na shiyyar Arewa-maso-Gabas da INEC ta tantance ya bayyana cewa zai tura jami’ai biyu a kowanne rumfunan zabe 69 domin sanya ido a zaben cike-gurbi na gwamnan jiha da za a yi ranar 18 ga watan Afrilu a jihar Adamawa.
Mukhtar Jada, kodinetan kungiyar ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Yola a yau Litinin.
Ya ce za’a baiwa jami’ansu dabarun sa ido tare da sanya ido kan yadda ake bin dokokin zabe da kuma tabbatar da cewa ba a yi magudin zabe ba tare da yiwa ‘yan takara adalci.
Mista Joda ya bayyana cewa kungiyar za ta kuma hada kai da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da hukumomin tsaro domin tabbatar da matakin da suka shirya na sake zaben ya gudana cikin nasara.
Ya kuma yi kira ga masu zabe a rumfunan zaben da ya shafa da su kasance cikin lumana, cikin tsari da kuma da’a a yayin gudanar da aikin, yana mai cewa zaman lafiya shi ne ginshikin ci gaban dan Adam.