Kakakin hukumar, Saminu Abdullahi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa, a wata tattaunawa ta wayar tarho a Kano cewa wani Umar Faruk Dalada ne ya bada rahoton faruwar lamarin da kuma inda ya faru.
Ya ce: “Lamarin ya faru ne a ranar 22 ga Afrilu, da misalin karfe 05:40 na yamma.
Ya ƙara da cewa akwai mutane 11 a cikin kwale-kwalen, an ceto shida da ransu, yayin da aka kwaso biyar babu rai.
“Sunayen wadanda suka rasa rayukansu a wannan haÉ—arin sune Abdulrazak Nabara, mai shekaru 40; Daha Muktar Atamma, 40; Mustapha Ibrahim, 45; Umar Isah mai shekaru 35 da Umar Idris mai shekaru 35,” inji shi.
PRO ɗin ya ce wadanda abin ya shafa sun fito ne daga unguwar Fagge da ke Ƙaramar Hukumar Fagge.
Ya ce an fara gudanar da bincike kan haÉ—arin kwale-kwalen kuma za a bayar da rahoton nan take bayan an kammala.