Aigbe ta bayyana hakan ne a wani taron lacca/ addu’o’i na musamman na Ramadan da ita da mijinta, Kazeem Adeoti su ka shirya a ranar Asabar.
Jarumar, wacce ta lashe kyautar gwarzuwar jarumai Nollywood ta kuma bayyana cewa sabon sunanta yanzu shine Meenah.
A wani faifan bidiyo na taron, wanda ya fito a jiya Lahadi, jarumar ta ce, “Insha Allahu, sabon sunana Hajia Meenah Mercy Adeoti. Meenah da H.”
Ta kuma nuna jin dadin ta ga bakin da su ka halarci laccar.
Jarumar dai ta auri Mista Adeoti ne a shekarar 2022 kuma an zarge ta da neman maza bayan da aurenta da tsohon mijin ta, Lanre Gentry.