Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Najeriya, NCDC, an samu barkewa annobar cutar amai-da-gudawa a jihohi shida da su ka haÉ—a da Cross River (397), Zamfara (25), Ebonyi (11), Abia (9), Bayelsa (3) da Kano (2), inda ake zargin mutane 447 sun kamu da cutar a cikin makonni 5 zuwa 9 na 2023.
Hukumar NCDC, ta shafinta na yanar gizo a yau Litinin, ta ce, duk da haka, jihohi 12 sun ba da rahoton bullar cutar, wacce ake kira da kwalara tun farkon shekarar 2023 - inda ta ce jihohi su ne Abia, Bayelsa, Benue, Cross River, Ebonyi, Kano, Katsina, Niger, Ondo, Osun, Sokoto da Zamfara.
Hukumar ta ce, ya zuwa ranar 5 ga Maris, jimillar mutane 922 da ake zargi sun kamu da cutar, ciki har da mutuwar mutane 32 (CFR 3.5%), daga Jihohi 12 a shekarar 2023, ciki har da Cross River (16), Ebonyi (shida), Abia (shida). , Niger (biyu), Zamfara (daya) da Bayelsa (daya).
Rahoton da NCDC ta fitar ya nuna cewa, a cikin dukkan johohin da da aka samu bullar cutar tun farkon shekarar 2023, jihar Cross River ce ke da kashi 70 cikin 100 na adadin wadanda suka kamu da cutar a fadin kasar nan, inda ta samu mutum 647.