Jam’iyyar ta yi wannan kiran ne a wani taron manema labarai da sakataren yada labaranta na kasa, Debo Ologunagba ya yi a Abuja a jiya Lahadi.
Ologunagba ya ce sakamakon da aka ɗora a na’urar IREv, tuni ya nuna cewa Fintiri ne ya lashe zaɓen.
“Saboda haka PDP ta bukaci shelkwatar INEC da ta gaggauta umartar jami’in zabe da ya kammala tattara sakamakon zabe, ya bayyana sakamakon zabe a rumfunan zabe tare da bayyana dan takararmu, Mista Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan da ya samu rinjayen kuri’un da aka kaɗa.Daga sakamakon da aka riga aka tattara a rumfunan zabe 69 da aka gudanar da zabukan karara wadanda ke kan na’urar IReV, Fintiri ne ya lashe zaben.
“Don haka jam’iyyarmu ta bukaci INEC ba tare da bata lokaci ba, ta bayyana sakamakon zabe kamar yadda aka riga aka tattara daga rumfunan zabe, sannan ta bayyana Fintiri a matsayin wanda ya yi nasara.Duk wani mataki da ba wannan ba to ba za mu yarda da shi ba kuma al’ummar Jihar Adamawa ba zai lamunta ba,” inji shi