A zantawar mu da Cmr. Adam Dakata na cibiyar wayar da kan al'umma kan kyakykywan shugabanci da adalci wato (CAJA) kan batun rushe guraren da gwamnati mai ci za tayi a kano ya bayyana mana ra'ayin shi tare da tambiɗi kan al'amarain
''A zahirin gaskiya ina goyon bayan alwashin da sabon Gwamnan Kano yaci akan rushe duk wani guri da akayi gini akan magudanan ruwa dakuma filaye da Gwamnatin Ganduje ta siyar wadanda bai dace asiyar dasu ba.
Sai dai kuma a matsayinmu na masu hankali idan muka kalli irin mawuyacin halinda wadanda suka mallaki irin wadannan filaye zasu tsinci kansu ya kamata a tausaya musu.
Sai dai koda kaji tausayinsu idan katuna cewa ba makafi bane su, sunsan abinda suka siya, saika gamsar da kanka cewa rusau din shine hanya mafi dacewa domin kawo sanity.
Misali : yanzu abin Allah ya kiyaye, ace gobara tatashi awasu bangarorin Kasuwannin Kofar Wambai da Kantin Kwari to saitayi mummunar barna kafin akasheta domin babu hanyar da Motar Kwana-kwana zata iya shiga domin kai tallafi.
Babu hankali da imani ga duk wanda ya yanka koya sayi shago afilin Masallacin Idi ko Masallacin Fagge da sauran manyan guraren ibada afadin Jihar Kano.
Bazamu manta da irin kiranye-kiranye, roko da magiya da irin su
Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa sukayiwa Gwamna Ganduje akan yayi hakuri karya sayarda filin dake gaban Gidan Zakkah da Hubusi, amma Gwamna bai amsa rokon nasu ba saboda yafi fifita bukatar Gwamnati akan ta Al’umma.
Bai dace ga duk mutum musulmi, Bahaushe, mai kishin kansa ya yarda ayanka Makaranta sannan shikuma yadauki kudi yasiya saboda yanajin shi mai arziki ne.
A ƙarshe, kirana ga mai girma sabon Gwamnan Kano da muka zaba; Engr. Abba Kabir Yusuf daya duba yiwuwar barin gine-ginen da akayi akan BUK Road domin sun kara fitoda hanyar fiyeda yanda take abaya''.