INEC ɗin ta sanar da Shehu, wanda aka fi sani da MB Shehu, a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike-gurbi da ya gudana a ranar Asabar.
Shehu ya lashe zaɓen ne da ƙuri’u dubu 19, 024, inda ya doke abokin karawar sa na jam’iyyar LP, Shuaibu Abubakar, wanda ya samu ƙuri’u 12,789, sai kuma ɗan majilasa mai ci, Aminu Suleman Goro, wanda ya zo na uku da ƙuri’u 8,669.
A yau ne dai INEC ta miƙa wa waɗanda su ka lashe zabukan na cike-gurbi shaidar lashe zabe a Abuja.Da aka zo kan Shehu, bayan da jami’ar ta miƙa masa tashi shaidar, sai ta miƙa masa hannu domin taya shi murna, inda shi kuma sai ya ƙi mika mata masa domin yin musabiha.
Daga nan ne dai sai Shehu ya dora nasa hannun a kirjin sa ya kuma rusuna domin girmamawa ga jami’ar.
Jaridar Raihana ta rawaito cewa haramun ne namiji ya yi hannu da macen da ba maharramarsa ba a addinin Musulunci