Jami'in sanar da sakamakon zaɓen gwamna na Adamawa, Farfesa Mohammed Mele ya ce Ahmadu Fintiri ya yi nasarar lashe zaɓen ne da ƙuri'a, 430, 861.
Gwamnan mai ci ya kayar da babbar abokiyar fafatawarsa Aisha Ɗahiru Binani wadda ta samu ƙuri'a, 398, 788.
Wannan nasara ta bai wa Fintiri ikon ci gaba da mulki a wa'adi na biyu.Da yammacin Talata ne, jami'in sanar da sakamako, Farfesa Mohammed Mele cikin rakiyar wasu manyan jami'an INEC na ƙasa, ya isa zauren karɓar sakamakon zaɓen da ke Yola, inda ya ci gaba da tattara sakamakon ƙananan hukumomin da suka rage.
A ranar 15 ga watan Afrilu ne, hukumar zaɓe ta gudanar da cikon zaɓen a wasu rumfuna da ke faɗin ƙananan hukumomin jihar 20.
Sakamakon zaɓen da aka ƙarasa dai ya nuna 'yar takarar jam'iyyar APC Aisha Ɗahiru Binani ta samu ƙuri'a 6,513, yayin Gwamna Fintiri na PDP ya samu
Sai dai zaɓen ya gamu da taƙaddama bayan kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa Hudu Ari ya sanar da Aisha Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen ba tare da ya fayyace sakamakon kowacce jam'iyya dalla-dalla ba.