Tinubu, wanda ya tafi kasar Faransa tun ranar 21 ga watan Maris, zai dawo Nijeriya ne kwanaki 35 kafin rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasar Nijeriya.
Da ya ke tabbatar da komawar sa Najeriya a yau Litinin, Onanuga, ya ce Tinubu zai dawo ne bayan makonni domin ya huta.
“A yau ne zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai dawo Abuja bayan ya shafe makonni yana hutu a kasar Faransa. E kabo! Se dada le de!, “in ji shi a cikin wata gajeriyar sanarwa.
Jaridar Raihana ta ruwaito cewa a watan Maris ne ofishin yada labarai na Tinubu ya bayyana cewa ya yi bulaguron ne domin ya huta da kuma yin shirye-shiryen tunkarar bikin rantsar da shi.Sanarwar ta kuma kara da cewa yayin da zai tafi, zababben shugaban zai kuma yi amfani da damar wajen tsara shirin karɓar mulki.
“Ya kuma umurci manyan mataimaka da ma’aikatan yakin neman zaben sa da su ma su je su huta. Ana sa ran zai dawo kasar nan ba da jimawa ba,”
Sanarwar ta kara da cewa, “Idan ya dawo kasar, ana sa ran zaÉ“aÉ“É“en shugaban kasar zai yi wasu tsare-tsare domin karÉ“ar mulki a ranar 29 ga watan Mayu,” in ji sanarwar.