Za a ga Watan Shawwal yau Alhamis kuma zai yi sama da mintuna 27 a samaniya, inji Sheikh Ibrahim Falaki
Malamin yace Watan Shauwal zai tsaya a yau Alhamis 20/4/2023 (Insha Allah), kuma zai samu sama da mintina 27 a sama bayan faÉ—uwar rana.
Yace kuma a neme shi daga É“angaren Arewa kaÉ—an da mafaÉ—ar Rana. Idan Allah ya nufa an ganshi, za a ganshi a kwance daga É“angaren Arewa da mafaÉ—ar Rana.