Majalisar wakilai ta gayyaci waɗannan ministoci guda biyu haɗe da gwamnan babban banki na ƙasa mr. Godwin emefiele domin yin bayanin yadda ba'asin yake amma abun ya faskara.
Gayyatar ta biyo baya ne tun bayan da masu binciken sirri suka sanar da badaƙalar dake faruwa tsakanin ministocin da babban gwamnan bankin ƙasa suka aikata.
Izuwa yanzu dai babu wanda ya amsa gayyatar a gaban ƴan majalisu kuma da yiwuwar kakakin majalisar yasa a kamo masa su a gurfanar dasu a gaban sa domin musu titsiye kamar yadda doka ta bashi dama.