Tauraron fina-finan ya ce dansa, Ahmad mai shekaru 16 shi kwallon kafa ya ke da ra’ayi, yayin da ‘yarsa, Fatima ke da sha’awar karatun alakar kasa da kasa a jami’a.
Nuhu ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa, inda ya ce yaran biyu sun fara samun nasara a fannonin da su ka zaɓa.
“Gaskiya na fi son ɗa na ya zama jarumi amma ya dage cewa shi kwallon kafa ya ke sha’awa, don haka na tallafa masa saboda a zamanin nan ba za ku iya tilasta wa yaranku a kan sana’ar da basu da ra’ayi ba.
“A matsayinka na uba idan ka gano abinda yaranka ke sha’awar yi a rayuwa, dole ne ka ƙarfafa musu gwiwa. A gare ni, na fi son in yi aiki da shi amma shi ba shi da ra’ayi.
“Fatima ta yanke shawarar kin yin wasan kwaikwayo tun tana shekara 13. Ta so ta karanci ilimin dangantakar kasa da kasa. Maganar nan da nake yi da kai, magana tana gab da kammala ahi uku a jami’a, kuma godiya ta tabbata ga Allah tare da kwarin gwiwarmu, tana cikin daliban da ke da Mali mafi yawa CGPA, a ajinsu.”
Jarumin ya ce an samu ci gaba, inda ya kara da cewa sana’ar na ci gaba da habaka cikin sauri, musamman ganin yadda Netflix da Amazon ke zuwa.