Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, shi aka zaɓa a matsayin shugaban majalisar dattawa na majalisa ta 10.
A makon nan ne dai kafafen yaɗa labarai su ka rawaito cewa zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince wa tsohon ministan na harkokin Neja-Delta ya zama shugaban majalisar dattawa.
Sai dai jam’iyyar APC mai mulkin kasar, bayan taron kwamitin koli na kasa na mako-mako a ranar Laraba, ta ce za ta yanke shawarar raba mukaman shugabancin majalisar dokokin kasar bayan tattaunawa da zababben shugaban kasa.
Amma a nasa bangaren, Ganduje, yayin da ya ke magana a wata ganawa da gwamnan jihar Cross Rivers, Ben Ayade, a Calabar a jiya Alhamis, ya ce matakin nadin Mista Akpabio ya riga ya gama aiki.Taron ya kuma samu halartar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari.
“Shugaban majalisar dattawan tarayyar Najeriya zai fito daga kudu maso kudu kuma ba wani mutum bane illa tsohon gwamnan Akwa Ibom,” inji shi.
“Ina ba ku tabbacin, muna jiran ranar rantsuwa kawai cewa zai zama shugaban majalisar dattawan Najeriya.”
A nasa bangaren, Mista Ayade ya nuna jin dadinsa da zabin Mista Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa,”