Wata kotun Majistare da ke Makurdi, a ranar Juma’a ta umurci wata matar aure, Doosu Samuel da ta share harabar kotun na tsawon kwanaki 21 saboda ta kwara wa wata yarinya Æ´ar shekara 15 ruwan zafi.
Ƴan sanda ne su ka kama Samuel wacce ke zaune a Logo 1, Makurdi da laifin haddasa mummunan rauni a karkashin sashe na 248 na dokokin penal code na jihar Benue, 2004.
Sai dai kuma Samuel ta amsa laifinta.
Alkalin kotun, mai shari’a Kelvin Banongo a hukuncin da ya yanke ya yi tir da wannan aika-aikar da wacce ake kara ta aikata.
Ya umurci mai laifin da ta riÆ™a share harabar kotun daga karfe 10 na safe zuwa rana daga Juma’a zuwa 5 ga watan Yuni, a kullum banda ranar Lahadi.
Alkalin kotun ya kuma umurci magatakardar kotun da ya tuntubi jami’an gidan gyaran hali da ke Makurdi domin kulawa.
Tun da fari, Lauyan masu shigar da kara, Insp Omayi Ujata, ya shaida wa kotun cewa ‘yan sanda sun samu kiran waya daga Ene Terwase a ranar 7 ga Mayu, 2023.
Ujata, ya ce wanda ya shigar da korafin ya shaidawa ‘yan sanda cewa mai laifin ta zubawa ‘yarta, Mimidoo Samuel ruwan zafi ba tare da wani dalili ba kuma ta raunata ta.
Ya ce ‘yan sanda sun garzaya da yarinyar da lamarin ya rutsa da ita zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Binuwai inda har yanzu take jinya.