Kwai na daya daga cikin abincin da masana ke bada shawara ga mutane musamman maza suci kafin kusanci.
Kwai wani abinci ne na asali a yawancin al'adu na duniya, kuma saboda kyawawan dalilai.
Wadannan abubuwan al'ajabi masu cike da fa'idojin kiwon lafiya da yawa waɗanda zasu iya inganta lafiyar gaba da samar da walwala.
A cikin wannan yanki mai layi da ɗabi'ar "Layin Lafiya", zamu duba tasirin kwai a rayuwar ku ta jima'i.
Ku biyo mu......
A cewar masu bincike a cikin bututun gwaji da dabbobi, selenium yana taimakawa wajen haɓbaka samar da hormones na jima'i (testosterone) ta hanyar kunna wasu hanyoyi da bayyanar wasu kwayoyin halitta.
Bugu da ƙari kuma, nazarin ɗan adam ya gano cewa matakan testosterone sunfi girma a cikin waɗanda keda matakan selenium mafi kyau a cikin jininsu.
Don haka, mutanen dake cin ƙwai akai-akai sukan sami babban selenium fiye da waɗanda basu ci ba.
Ana ganin cewa ha'ila yau ƙwai kuma na iya taimakawa wajen kwararar jini zuwa al'aurar wanda hakan ke nufin yana iya rage haɗarin lalata farji da gaba.