A wani mataki da masu sharh ke gani a matsayin hukunci, an mayar da Mista Isah, Sufeton ‘yan sanda zuwa hedikwatar ‘yan sandan shiyya ta 14 da ke jihar Katsina.
Sabbin canje-canjen wajen aiki, a takarda mai kwanan wata ranar 25 ga Mayu, 2023 kuma mai taken CH.5360/FS/FHQ/ABJ/V.Til/210, ya shafi jami’an yansanda 15, inda Mista Isa ke kan gaba.
A baya-bayan nan wata ‘yar jarida a Katsina, Rukayyah Jibia, ta yi ƙorafi kan barazanar da ƴansanda suka yi mata, bayan ta wallafa wani faifan bidiyo a TikTok, inda ta caccaki rundunar ƴansandan jihar Katsina bisa nuna masu kaifi a bidiyo tun kafin a kai su kotu.
Ta ce gurfanar da wadanda ake zargin na iya bata sunan su, musamman idan ba a same su da laifi ba aka sallame su sannan kotu ta wanke su.
Ta kuma bukaci ‘yan sanda da su rika baiwa kotu damar hukunta wadanda ake tuhuma ko kuma ta yanke musu hukunci kafin mika su ga manema labarai.
Sai dai waɗannan kalamai na Jibia ba dhyi wa ƴansandan dadi ba, inda suka zarge ta da raina aiki da kuma katsalandan a aikin su.
Ta kara da cewa yanzu haka tana ɓoye ne a wani waje bayan da ƴansanda su ka kai koken ta wajen Sarkin Katsina, wanda ya kuma bada umarnin a ci gaba da tsare ta a hannun yansanda.
Sai dai kuma bayan nan, yayin da aka bada belin ta, sai ta tsere Bayan da ƴansanda su ka nemi ta koma washegari.
Da aka tuntubi tsohon kakakin ƴansandan, Gambo Isah ya musanta zarge-zargen.