Angola ta tserewa Najeriya a matsayin ƙasar da ke kan gaba wajen fitar da ɗanyen man fetur a Afirka.
Wani rahoton da kungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur ta OPEC ta fitar, ya nuna cewa Angola na fitar da ganga miliyan 1.06 na man fetur a kowacya ragu daga ganga miliyan 1.3 a rana zuwa 999,000 a watan Afrilun 2023, inda ya yi ƙasa da kashi 23.
OPEC ta ce ƙasashen da aka samu ƙaruwar ɗanyen man fetur da suke fitar wa, sun haɗa da Saudiyya da Angola da kuma Iran, yayin da aka samu raguwa a Iraqi da Najeriya.
Haka ma, bayanai daga hukumar kula da harkokin mai a ƙasar, sun nuna cewa an fara samun raguwa a mai da Najeriyar ke samar wa cikin watanni uku na farkon wannan shekara.
Najeriya wadda ke da karfin samar da ganga miliyan 2.2 na man fetur, ta sha fuskantar matsaloli musamman ma na ayyukan masu satar ɗanyen man fetur da fasa bututai da kuma rashin sabbin masu zuba jarin a ɓangaren.