Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Musa A. Lawan yaÆ™i Æ™aryata rahotannin da kafafen yaÉ—a labarai suke fitarwa dake nuna cewa kotu ta tilasta masa ya gurfanar da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai
Hon Alhassan Ado Doguwa a gaban kuliya.
Baya ga haka, babban lauyan jihar ya damu da yadda mai karar ya kasa gabatar da bukatar da wata babbar kotun jihar ta bayar a gaban jama’a yadda ya kamata, kuma da gangan ya gwammace yayi shiru don yaudarar jama’a a kan shari’ar Doguwa.
Mai shari’a Maryam Sabo Mni a ranar 26 ga Afrilu, 2023 ta bada izinin biyan buÆ™atun da Babban Alkalin Kotun Mai shari’a Muktari Dandago mai ritaya ya shigar dashi na tilastawa babban lauyan gurfanar da wanda ake zargi da aikata laifuka kamar haka:
Kisan kai, hada baki da wasu don aikata sauran laifuka.
wasu kafafen yaÉ—a labarai da suka karyata umarnin kotun sun ruwaito cewa
an tilastawa AG na Kano gurfanar da wanda ake tuhuma.
“Babu wani umarni na MANDAMUS da aka bani, kuma idan lauyoyin masu Æ™ara zasu cigaba da zama kwararru ya kamata su dunga faÉ—ar gaskiyar lamari ba sabanin haka ba, kuma su dunga cire ra'ayin siyasa yayin gufanar da ayyukan su, su kuma cigaba da bayyanawa jama’a gaskiyar abin da umarnin ya bayar a zahiri. Da kuma abunda umarnin ya Æ™unsa.
“Lauyoyin da suka shigar da karar sun san cewa batun ba gaskiya bane amma sun yanke shawarar yin shiru ne saboda siyasa, takardar da aka shigar a gaban kotun dama ce in bayyana a gaban kotu domin in bayyana dalilin daya sa baza a tilasta ni in gurfanar da Doguwa a gaban kotu ba.
Barista Lawal ya zanta da manema labarai a ranar Litinin da ta gabata lokacin da ya bayyana dalilin da ya sa ba za a tilasta masa gurfanar da dan majalisar tarayya mai wakiltar Doguwa/Tudun- Wada ta Kano a gaban majalisar wakilai ba." mun zauna ranar juma'a amma hakan bai ci tura ba sai aka dage shari'ar zuwa ranar litinin wato yau kuma dalilin da yasa muka zo nan tun karfe 9 na safe aka ce mana shari'ar baza ta cigaba ba saboda alkali bai dawo ba.
“A shirye muke mu kare kanmu, kuma ina fata wannan bada nufin jinkirta shari’ar ba ne ko kuma a cigaba da sauraren shari’ar idan ba'a saurare mu ba, kuma a yanzu za'a tuhume mu da rashin zuwa gaban kotu, saboda kotu ta basu izinin bayyana. don bayyana dalilin daya sa a oda tawa.
Kada a bada mandamus a kanmu kan tuhumar Doguwa.” A cewar AG. A halin da ake ciki kuma, shari’ar da aka shirya yi ranar Litinin ba ta cigaba ba, saboda rashin halartar mai shari’a Sabo da aka ce zai je kotun sauraron kararrakin zabe a jihar Adamawa.
Source