Bola Ahmed Tinubu, yayi alƙawarin yiwa ƙasa ayyukan cigaba dai-dai wa dai ba tare da nuna wariya ga wani ɓangare na ƙasar ba.
Tinubu, wanda za'a rantsar dashi a matsayin shugaban ƙasa a ranar 29 ga Mayu, ya bayyana hakan ne a jiya Laraba a Phorthacourt babban birnin jihar Rivers
A sanarwar da Abdulaziz Abdulaziz, mataimaki ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai ya aikowa
Jaridar Daily Nigerian Hausa a yau Alhamis, Tinubu ya fadi hakan ne yayin ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar, domin ƙaddamar da ayyukan da gwamnatin Nyesom Wike ta aiwatar.
“Ba zan mayar da wani yanki saniyar-ware ba, hasali ma, zan bar ayyukan da ba za a manta da su ba a faÉ—in Nijeriya,” in ji shi a yayin buÉ—e gadar Rumuokwuta/Rumuola.
Tinubu ya yabawa Gwamna Wike bisa ayyukan ci gaba da ya cimma a jihar Ribas, musamman gadar sama 12 da aka gina a faɗin babban birnin jihar, inda ya ce lallai tarihi zai riƙa tunawa da shi.
Ya ce da irin nasarorin da ya samu a jihar, Nijeriya za ta buÆ™aci gwamnan Ribas É—in mai barin gado a manyan muÆ™amai.É“angaren siyasa, Tinubu ya godewa Wike da al’ummar jihar Ribas bisa goyon bayan da suka ba shi.
Ya ce yana jihar ne bisa alÆ™awarin da ya É—auka a lokacin yaÆ™in neman zaÉ“e a Ribas, inda ya ce “idan ka yi alÆ™awari, ka cika shi.
“Ba zan taÉ“a mantawa da muhimmiyar rawar da manya da kuma al’ummar jihar nan suka taka ba a yaÆ™in neman zaÉ“en da na yi na zama shugaban Æ™asar nan. Kuna da godiyata ta har abada.
A mai girma Gwamna Wike, na ga mutum mai Æ™a’ida. Ya É—auki matakin da ya dace na cewa a mayar da shugabancin Æ™asarnan Kudu, kuma ya samu Æ™warin guiwar jajircewa kan matsayarsa, ba tare da la’akari da wa hakan zai É“atawa ba.
“HaÆ™iÆ™a shi mutum ne mai mutunci. Bai zaÉ“i biyan buÆ™atar kansa ba, a’a, ya zaÉ“i biyan buÆ™atar Æ™asa da al’ummar jihar Ribas, ina gode masa bisa wannan jagorancin na sadaukar da kai,” inji shi.
A nasa jawabin, Wike ya ce gayyatar da aka yi wa Tinubu domin ƙaddamar da ayyuka a jihar cika alƙawari ne da aka yi a ziyarar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a Rivers
Ya kuma godewa Tinubu kan yadda ya amince ya ziyarci jihar Rivers tare da ƙaddamar da ayyukan.
Wike, wanda ya caccaki shugabannin jam’iyyarsa ta PDP, ya yaba da zaÉ“en Tinubu wanda a cewarsa, ya kunyata masu zagon Æ™asa.
Taron ya samu halartar Kakakin majalisar wakilai Hon. Femi Gbajabiamila da Gwamna Abubakar Badaru (Jigawa), David Umahi (Ebonyi), Abdulrahman Abdulrazaq (Kwara), Seyi Makinde (Oyo) da Hope Uzodinma (Imo).
Sauran sun haɗa da tsoffin gwamnoni Dr Odili (Ribas), Cif Bisi Akande (Osun), Cif James Ibori (Delta), Dr Kayode Fayemi (Ekiti), Cif Timipre Sylva (Bayelsa) da Cif Ayo Fayose (Ekiti). Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da zaɓaɓɓen gwamnan jihar Ribas, Mista Sim Fubara, Ministan matasa da ci gaban wasanni, Mista Sunday Dare, Mista Dele Alake da kuma Alhaji Kashim Ibrahim Imam, da dai sauransu.