Shugaban Æ™asa Bola Tinubu zai fara aikinsa a matsayin shugaban Najeriya da ganawa da gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele da luma Babban Jami’in Rukunin Kamfanin Man Fetur na Najeriya Limited, NPL, Mele Kyari.
Duk da cewa ba a bayyana makasudin taron a hukumance ba, jaridar RAIHANA ta ruwaito cewa taron ba zai rasa nasaba da rikicin da aka samu na kawar da tallafin man fetur wanda tun daga lokacin ya jefa ‘yan Najeriya cikin fargaba.
Tinubu ya isa fadar shugaban kasa a yau Talata da misalin karfe 2:30 na yamma, inda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da wasu manyan jami’an gwamnati suka tarbe shi a kofar ofishinsa.
Sauran wadanda su ka halarci taron sun hada da kakakin majalisa, Femi Gbajabiamila da babban sakataren majalisar dokokin jihar Tijjani Umar, tsohon kwamishinan kudi na Legas, Wale Edun; Dele Alake; James Faleke.