Abiodun Oladunjoye, Daraktan (Bayanai), fadar shugaban ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Asabar a Abuja.
A cewar sanarwar, an samar da kayayyakin kiwon lafiya na zamani ga asibitin, wanda zai amfani al’ummar unguwar Hotoro, musamman mata da yara.
“Hukumar ci gaba mai dorewa, ofishin SDGs a fadar shugaban kasa ce ta sanya shi cikin ayyukan ta, sannan aka gabatarwa gwamnatin jihar Kano ta karba, wanda nan take gwamnatin Ganduje ta amince da yin hakan.
“Kazalika, gwamnatin jihar ta kuma daidaita da al’ummar yankin da su sanya wa asibitin suna ‘Fatima Shehu Maimota Clinic’, domin karrama mahaifiyar babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Malam Garba Shehu, wanda shima dan unguwar ne”.
A ranar Lahadi ne da karfe 2 na rana za a kaddamar da asibitin.
Ana sa ran ginin zai samar da kayayyakin jinya na zamani ga mata da yara a jihar.