Ganduje yayi aiki a kano amma idan aka bayyana muku ta'asar da yayi da satar da yayi a kano ko kare bazai ci ba.
Tun farko idan kuka duba ayyukan sa na kaddamar da asibitin yara na gwamna shekarau a farkon tenuar sa da yayi abu ne mai kyau kuma dashi ya fara jan hankalin mutanen kanawa sukai zaton zai ɗora kan abubuwa na ƙwarai da muka bari a baya. Ya ƙarasa gadoji kuma ya biya wasu daga cikin basussuka na kuɗin karatun ɗalibai da ake bin mu a ƙasashen ƙetare amma wasu bai biya ba sai haƙura sukai da karatun wasu suka dawo gida wasu kuma suka zauna domin nemawa kansu mafita.
Abu na farko daya fara yi wanda ya fito da halayyar sa ta makirci da maitar kuɗi a cikin irin halin sa na son Duniya, kwatsam sai aka gano shi a faifan bidiyo yana karbar daloli a gurin ƴan kwangila wanda hakan ya nuna cewa ba wannan ne farau ba illa iya ka dai Allah ne ya nunawa jama'ar kano asalin halin sa. Azzalumi ne ƙwarai da gaske kuma halayeb sa sun fito ƙarara daga wannan lokaci inda ya fara cin mutuncin mutanen kirki yana tafiya da maras ya ɗora uwar ɗakin sa kan ragamar komai na tafiyan tar d mulki a kano, ya cefanar da dukiyoyin jihar kano, ya toshe duk wata mafaka da ɗalibai zasu bi domin jin dai a jihar kano mussaman a makarantun su da suke jaratu na yau da gobe duk da cewa yara suna bukatar wasa ƙwaƙwalan su domin karatu ya shige su kuma su fahimci inda aka dosa yayin ɗaukar darasi.