Dr. Abdullahi Umar Ganduje ba zai halarci wajen bayar da mulki ba wanda za’ayi a gobe a filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai mai barin gado, Mallam Muhammad Garba ya fitar, yace gwamnan zai bayar da mulki ne a yau da misalin karfe 9 na dare a gidan gwamnati.
A cewar kwamishinan, kwamitin bayar da mulki ya tattauna da kwamitin karbar mulki na sabuwar gwamnati mai zuwa kuma sun tsara yadda komai zai kasance.
Mallam Muhammad Garba yace bayan gwamnan ya bayar da mulki zai tafi babban birnin tarayya Abuja domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu.
A karshe yayi kira ga al’umma jihar Kano da su cigaba da yiwa jihar Kano addu’a domin samun ci gaba.