Da ta ke jawabi yayin karɓar kashin farko na ƴan Nijeriya 376 da su ka makale a kasar Sudan da yaki ya daidaita a filin jirgin saman Abuja, Ministar ta kuma bayyana cewa gidauniyar MTN ta bayar da gudunmuwar 25GB na data da katunan waya na Naora dubu 25 ga kowane daya daga cikin wadanda aka kwaso din.
A cewarta, tallafin na Naira dubu 100 da gidauniyar Dangote ta bayar, an ba wa waɗanda aka kwaso din ne domin su yi amfani da kudin a matsayin kudin mota zuwa gidajen su cikin sauki.Shima da ya ke nasa jawabin, jakadan Sudan a Najeriya, Mohammad Yusuf yace nan bada jimawa ba za’a shawo kan yaƙin na Sudan.
Yusuf ya nuna farin cikinsa da yadda Najeriya ta samu nasarar kwaso ‘yan kasarta lafiya.
Wakilin, wanda ya bayyana Sudan a matsayin kasa ta biyu ga yawancin ƴan Nijeriya, ya ce nan ba da jimawa ba za a dawo da zaman lafiya a kasar da yaki ya fara daidaitawa.