Gwamnatin jihar Kano ta biya bashin tallace-tallace sama da Naira miliyan 500 da ta gada a cikin shekaru takwas da su ka gabata.
Kwamishinan yaÉ—a labarai da harkokin cikin gida na jihar mai barin gado, Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a jiya Juma’a a Kano yayin da ya ke mika ragamar ma’aikatar ga babban sakatare, Sani Yola.
Malam Garba ya bayyana cewa basussukan sun taso ne daga tallace-tallacen da aka sanya a kafafen yada labarai daban-daban, wadanda ya gada bayan hawansa mulki.
A cewarsa, an sake farfado da ma’aikatar a lokacin da ya ke rike da mukamin, wanda hakan ya sanya sama da jami’ai 35 su ka samu Æ™arin matsayi zuwa daraktoci tare da daukaka matsayin ‘yan jarida guda biyar daga ma’aikatar zuwa mukamin sakatarorin dindindin a ma’aikatar.
Malam Garba ya kara da cewa kamfanin buga jaridu na gwamnatin jihar, Triumph, ya farfado ta hanyar samo sabbin injinan bugu na kamfanin da kuma tabbatar da buga jaridun nasa da dai sauransu.
Ya kuma ce gwamnatin jihar ta gina shaguna 24 a sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ, tare da sabunta dakin taro na sakatariyar domin ba ta damar samun kudaden shiga domin gudanar da ayyukanta.