A cikin wata sanarwa da hukumar ta CAA ta fitar ta ce jirgin ya yi saukar gaggawar ne da yammacin jiya Litinin a filin jirgin sama na Jinnah na Karachi bayan wata mata mai juna biyu, ƴar kasar Philippines ta da naƙuda.
Hukumar ta CAA ta ce an ba matar agajin farko a cikin jirgin, inda ta kara da cewa likita da motar daukar marasa lafiya sun kasance a lokacin da jirgin zai⁴ sauka, yayin da aka haifi yaron a lokacin.
Sanarwar ta ce an kai matar da yaronta zuwa asibitin yankin, kuma jirgin ya tashi cikin sa’o’i biyu da sanyin safiyar Talata.
Jirgin ya taso ne daga Doha zuwa Manila, a cewar CAA.