Sakamakon binciken da aka buga a cikin Mujallar Zuciya ta Turai – Digital Health, ESC, an buga shi akan Yanar Gizo na ESC a jiya Juma’a.
Binciken da Farfesa Xianhui Qin na Jami’ar Kiwon Lafiya ta Kudancin Guangzhou na kasar Sin ya rubuta, ya ce yana da kyau a takaita kiran wayar hannu don kiyaye lafiyar zuciya.
“Yawan mintunan da mutane ke kashewa suna magana akan wayar hannu na da tasiri ga lafiyar zuciya. Ƙarin mintuna na yin waya na nufin haÉ—ari.
“Amma idan za a debi shekaru ana yin waya ta amfani da sautin ta ta waje, hakan ba zai yi wani haifar da cutar hawan jini ba
“Ana buÆ™atar Æ™arin nazari don tabbatar da sakamakon binciken,” in ji shi.