Ƙusa a jam'iyyar APC a jihar Kano, Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya yi kira ga ƴan jam'iyyar da su daina yaɗa farfaganda cewa ba za a rantsar da Abba Kabir Yusuf na jam'iyar NNPP a matsayin gwamnan Kano a ranar 29 ga watan Mayu ba.
Da ya ke jawabi a wajen wani taron siyasa, wanda Rahma Radio ta saka a shirin ta na "Harshen ka Alkalin ka" a jiya Alhamis, Danzago ya nuna takaicin yadda ƴan jam'iyyar ta sa ta APC ke yaɗa jita-jita a kan nasarar zaɓe da Abba ya samu a zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris.
A cewar sa, yaɗa irin wadannan jita-jita abin kunya ne kuma masu fadin hakan na kunyata jam'iyyar a idon ƴan adawa.
Zago, wanda aka fi sani da Danzago, ya ce duba da tanade-tanaden kundin tsarin mulki na kasa da dokokin zaɓe, babu abinda zai hana a rantsar da Abba a ranar 29 ga watan Mayu sai dai mutuwa ko juyin mulki.
Sai dai ya yi kira ga magoya bayan jam'iyyar APC da su kwantar da hankalinsu su jira matakin shari'a da jam'iyyar ta dauka na ganin cewa ta kwato hakkinta a kotu.
A cewar sa" ko kotun ma da ake magana, wato tribunal, har yanzu ba ta fara sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna a Kano ba. Irin waɗannan jita-jita da ake yaɗa wa, ma su yi mu kunyata mu su ke yi.
"Ba yadda za a yi a ce ba za a rantsar da Abba ba sai dai in hali na mutuwa ko juyin mulki. A bari a rantsar tukuna, in ya so sai a bi mataki na kotu.
"Ko an je kotun ma, har yanzu fa tribunal ba ta fara sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna ba. In ma an yi, to fa sai an je appeal court daga nan kuma a wuce Kotun Ƙoli. Ko mu kai su, ko su kai mu,.
Kawai dai mu ci gaba da addu'a mu kuma kwantar da hankalin mu," in ji Danzago.