Lamarin ya afku ne a jiya Laraba da misalin ƙarfe 5 na yamma a layin Karshen Kwalta da ke unguwar Rimin Kebe a ƙaramar hukumar Ungoggo
“Ina tsaye a kofar gidana, kwatsam na ji ihu daga gidan marigayiyar,” wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa manema labarai.
Ya bayyana cewa da ya garzaya wajen domin ganin me ka faruwa, sai ya tarar da mahaifiyar, wacce ya daddaɓawa wuƙar a gurare daban-daban, na kwance cikin jini, tana neman agaji.
Ya bayyana cewa wanda ake zargin ya gudu daga wurin jim kadan bayan ya aikata ta’addancin ga mahaifiyarsa.
Shaidan ya ci gaba da cewa daga baya an garzaya da matar zuwa asibiti a Babur din adaidaita sahu, inda daga bisani likitoci su ka tabbatar da rasuwar ta.
“Tun jiya aka yi jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Allah ya gafarta mata, ya shigar da ita aljannah,”
Da aka tuntubi kakakin rundunar Æ´ansanda ta Kano , Abdullahi Haruna, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma yi alkawarin bayar da cikakken bayani nan gaba kadan.