Ministan wutar lantarki, Abubakar Aliyu, wanda ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da wutar lantarki a karkashin jagorancin Sanata Gabriel Suswam, yayi nuni da cewa bankin Exim na China da gwamnatin Najeriya ne ke É—aukar nauyin aikin wutar na dam din Zungeru.
Ya kuma yi nuni da cewa, anbi duk wani kyakkyawan tsari da ka’idoji don tabbatar da cewa Najeriya bata yi asara ba a cikin yarjejeniyar.
Aliyu ya bayyana cewa har yanzu ayyukan samar da wutar lantarki mallakin gwamnatin tarayya ne, kuma wannan jinginar ta tsawon shekaru 30 ne kawai.