Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada mataimakin babban sufeton ƴansandan Najeriya, Garba Umar mai ritaya a matsayin babban mai ba da shawara kan harkokin tsaro a harkokin yansandan na duniya da kuma yaƙi da ta’addanci a ofishin ministan harkokin ƴansanda.
Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa a yau Alhamis a Abuja.
Shugaban ya ce naɗin na da nufin baiwa Najeriya damar ci gaba da rike muhimman mukami da kuma bai wa Umar dama ya kammala wa’adinsa na bauta wa kasa a matsayinsa na mamban zartarwa na kungiyar yansanda ta kasa da kasa, INTERPOL.
Da ya ke amincewa da nadin nasa, Buhari ya yi la’akari da wani misali da gwamnatin tarayyar Najeriya ta ci gaba da rike tsohon mamba mai ritaya, AIG Kamal Subair, bayan ya yi ritaya a shekarar 2018.
Shugaban ya kuma lura da cewa, a lokacin da Umar ya ke mamba a kwamitin zartarwa, ya taimaka wa Nijeriya ta fannoni da dama, tare da fatan nan da shekara daya da ta rage, zai kara yin kokari wajen samar da kayan aiki na daƙile laifuka, da kula da iyakoki da kuma yaki da ta’addanci ga kasar.
A cewarsa, ana kuma sa ran Umar zai taimaka wajen ganin an samu karin ‘yan Najeriya a manyan mukamai a INTERPOL.
AIG Umar zai kammala zangon aikin sa a INTERPOL a watan Nuwamba 2024, kuma sabon nadin nasa a matsayin babban mai ba da shawara kan harkokin tsaro zai fara aiki daga ranar 16 ga Mayu, 2023.