Kotun tsarin mulki a Uganda ta soke dokar da ta haramta amfani da muggan kwayoyi, irin su tabar-wiwi da ganyen khat.
Hakan dai ya biyo bayan kalubalen da kungiyar manoman ganyen khat ta soma yi na tsawon shekaru shida da suka gabata a matsayin martani ga dokar shekarar 2015.
Yanzu dai an soke dokar baki-É—aya bayan da kotu ta ce an zartas da shi ba tare da samun rinjaye Æ´an maajlisa da ake bukata a majalisar.
Kafin a yi muhawara da kuma zartar da doka a majalisar dokokin Uganda, dole ne akalla kashi É—aya bisa uku na dukkan mambobin da ke da hakkin kaÉ—a kuri'a su kasance a majalisar.
Ko da yake an soke dokar a yanzu, duk da haka akwai haɗarin cewa za a kama masu noma da sha ko kuma sayar da haramtattun kwayoyi a ƙarƙashin wasu dokokin Uganda.
A Uganda, jami’an tsaro sun kasance suna kai samame tare da Æ™ona gonakin da ake nome tabar-wiwi ko kuma ganyen khat.
A duk faɗin Afirka, ƙasashe suna yin yunƙuri don halatta kasuwanci da kuma fitar da tabar wiwi.
BBC