Hukumomin Saudiyya sun kama wani ɗan Najeriya ɗaya da ‘yan Saudiyya uku bisa zargin safarar hodar ibilis da ta kai nauyin kilogiram 2.2 a ƙasar.
BBC ta rawaito cewa sshen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan ƙasar ya ce ya samu nasarar daƙile yunƙurin shigar da hodar ibilis zuwa biranen Riyadh da Jeddah.
Ƴan sandan sun ce mutanen huɗu sun daɗe suna aikata laifin safarar hodar ibilis ɗin tare da sayar da ita a cikin ƙasar ta hanyar amfani da wasu miyagun dabaru.
Jami’an ‘yan sandan sun ce za a gurfanar da mutanen a gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike.
Safarar ƙwaya dai babban laifi ne a Saudiyya da za a iya yanke wa mutum hukuncin ɗaurin shekaru masu yawa a gidan yari, ko ma ta kai ga an fille wa mutum kai.
Daily Nigeria