Tijjani Gandu ya haɗu da haɗari a hanyarsa ta tafiya gida bayan ya dawo daga wajen aiki da daddare, izuwa yanzu dai yana asibiti rai kwakwai mutu kwakwai. Wakilin mu yayi ƙoƙarin jin ta bakin makusantan sa amma izuwa yanzu basu magantu ba kasancewar suna cikin matsanancin halin damuwa na yanayin da suka tsince shi a ciki.
Wannan dai ba shine karo na farko da haɗari ya faru ga manyan mabiya ɗarikar kwankwasiyya ba tun bayan da aka sanar da ABBA GIDA-GIDA a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar kano ba, domin satin daya gabata ma an samu masu take Abban baya sunyi haɗari inda ɗaya daga cikin su ya mutu har lahira.
RAIHANA