Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta cafke wani yaro dan shekara 16 mai suna Emmanuel John bisa kashe mahaifinsa, Monday John.
Wakilinmu ya tattaro cewa Emmanuel, da misalin karfe 10 na daren ranar Talata, 2 ga watan Mayu, ya yi amfani da tabarya wajen kashe mahaifinsa.
Lamarin dai ya faru ne a lokacin da ake takun saka tsakanin mamacin da mahaifiyar Emmanuel, Mrs Mercy John.
Wata majiyar Æ´an sanda ta bayyana cewa wani Yusuf Ayuba ne ya kai karar ofishin ‘yan sanda bisa jin Æ™arar Monday John a gidan a ranar Laraba, 3 ga watan Mayu.
A cewarsa, Emmanuel yana hannun Æ´ansanda kuma za'a gurfanar dashi a gaban wata kotu bayan an kammala bincike. Da yake tsokaci kan lamarin yayin ganawa da manema labarai a ranar Juma’a, kwamishinan Æ´ansandan babban birnin tarayya, Haruna Garba, yace wanda ake zargin ya bugi kan mahaifinsa da tabarya da Æ™arfi.
Garba ya ce, “Abin ya faru ne a lokacin da mahaifin ke dukan mahaifiyar matashin
“Wanda ake zargin ya koma gefe da mahaifiyarsa inda ya yi amfani da wata kwarya-kwaryar dukan iska da muciya kan mai uwa da wabi wanda a karshe yayi sanadiyyar mutuwarsa bayan ta same shi a kai''
Za'a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotun matasa idan bayan an kammala binciken