Dan majalisar wakilai ta ƙasa mai wakiltar karamar hukumar Dala daga jihar Kano, Aliyu Sani Madaki, ya bukaci gwamnatin tarayya ta samar da matakan rage radadi ga al'ummar Nigeria, bayan cire tallafin Man Fetur da shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yayi a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2023, a yayin da yake karɓar rantsuwar kama aiki.
Madaki yayi kiran a ranar Laraba yayin zaman majalisar ta wakilai, inda yace ya lura da yadda wasu al'ummar ƙasar ke shan wahala wajen gudanar da rayuwa tun bayan ayyana cire tallafin Man Fetur da shugaban ƙasa yayi, wanda har ta kai ga kayayyakin amfanin yau da kullum sun ƙara tsada, hakazalika wasu jihohin sun rage kwanakin aiki daga kwanaki biyar zuwa uku, duk saboda tsadar Man Fetur, inji shi.
Bugu da ƙari, Madaki ya ce hatta ƙungiyar kwadago ta ƙasa, ta so tsunduma yakin aiki kafin daga bisani ta janye, kuma Man Fetur din har yanzu babu tsayayyen farashi a wajen yan kasuwa.