Rundunar ƴansandan ta gurfanar da Dauda, mazaunin EFAB Global Estate, Life Camp, Abuja da laifin sata.
Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin.
Lauyan masu shigar da kara, Stanley Nwafoaku, ya shaida wa kotun cewa a ranar 26 ga watan Mayu da misalin karfe 9:05 na safe, Bolaji Olufumi, da ke unguwar Prosper Road Area 3, Abuja, ta shigar da ƙorafi a ofishin ƴansanda na Life Camp.
Nwafoaku yace, a ranar 20 ga watan Mayu, wanda ake kara ya gayyaci mai karar zuwa gidansa da ke a Estate EFAB, kuma bayan da ya kwanta da ita, sai ya sibare jakarta mai dauke da kudi Naira dubu 92,300.
Yace duk kokarin da Olufumi ta yi na karbo jakar da kudinta daga hannun wanda ake tuhuma ya ci tura.
A cewar sa, laifin ya saɓawa sashe na 288 na dokar hukunta manyan laifuka.
Alkalin kotun, Muhammed Wakili, ya bada belin wanda ake tuhumar a kan kudi naira dubu 100,000 da kuma mutum daya da zai tsaya masa.
Wakili ya ce dole ne wanda zai tsaya masa ya bada lambar BVN, hoton fasfo na sabo da kuma ingantaccen katin shaida, wanda magatakardan kotu ya tabbatar da hakan.