Babban sakataren yada labarai na gwamnan, Emmanuel Ogbeche ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, inda ya bayyana cewa haramcin ya biyo bayan tattaunawa da shugabannin hukumomin tsaro a jihar.
A cewar sanarwar, an taƙaita ayyukan acaɓa ne a unguwannin gefe-gefen birnin ƙasar.
Gwamnatin jihar ta yi gargadin cewa duk wanda aka kama yana karya dokar, za a ƙwace babur din tare da hukunta wanda ya aikata laifin.
Gwamnatin jihar ta kuma yi gargadi a kan barnatar da dukiyoyin al’umma kamar fitulun kan hanya da masu bayar da hannu.