“Muna da yaƙinin za ka iya sauke nauyin da shugaban kasa ya dora maka, saboda kishin sa na son ci gaban kasa da hadin kanta, kuma .m⁰una da tabbacin zaka yi amfani da wannan sabon mukamin na shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa wajen cigaban al’ummar Nigeria baki daya”.
A wata sanarwa da daukacin yan majalisar na NNPP, bisa jagoranci Tijjani Abdulqadir Jobe, mai wakiltar mazaɓar Tofa/Dawakin Tofa su ka sanyawa hannu sun ce mukamin da aka baiwa shugaban majalisar an saka kwarya a gurbinta saboda gogewar da yake da ita.
“Muna fatan zaka yi amfani da kwarewar ka ta dan majalisa da kuma ta shugabancin majalisar da ka rike wajen gudanar da sabon mukamin da aka baka”.
Sanarwar da ƴan majalisar suka aikowa kadaura24 ta yi addu’ar Allah ya dafawa sabon shugaban ma’aikatan fadar shugaban ya bashi ikon sauke nauyin da shugaban kasa ya dora masa.
Jerin sunayen yan majalisar da su ka sanya hannu a sanarwar:
1. Hon Tijjani Abdulkadir Jobe
Wanda shi ne shugaban su
2 . Hon. Abdulmumini Jibril Kofa
(Mataimakin Shugaba)
3. Hon. Kabiru Alhassan
4. Hon. Garba Ibrahim Diso
5. Hon. Aliyu Sani Madaki
6. Hon. Abdullahi Sani Rogo
7. Hon. Sagir Ibrahim Koki
8. Hon. MB Shehu
9. Hon. MD Hassan
10.Hon. Rabi’u Yusuf
11. Hon. Mukhtar Umar Zakaria
12. Hon.Hassan Shehu Hassan
13. Hon. Ciroma Muhd Nalaraba
14. Hon. Ghali Mustapha Tijjani
15. Hon. Idris Dankawu
16.Hon. Sani Adamu wakili
17. Hon. Yusuf Umar Datti
18. Hon. Abdulhakeem Kamilu