Gwamnan Kano Engr Abba Kabir Yusif, ya jagoranci rushe ginin sansanin Alhazai na Hajji Camp, da akayi ba bisa Ka'ida ba.
Gwamnan wanda tun a ranar Juma'a, daya ziyarci wannan sansani ya dauki Alwashin dawo da martabar wannan waje.
Da misalin karfe 2 na dare aka fara gudanar da wannan aiki na rushe wadannan gine gine, wanda sai da aka tabbatar an kammala komai.
Abba Bala Wanda Mazaunin wannan waje ne, ya bayyana yadda hakan ya kasance abin farin ciki a gareshi, saboda yadda a baya suna zaman su kawai aka tashe su.
A wani labarin kuma Gwamnan Kano Engr Abba Kabir Yusif, ya jagoranci rushe ginin Daula hotel dake shataletalen Rawul din Bompai.
A safiyar wannan ranar ce dai aka soma wannan aiki na tabbatar da ganin an dawo da hakkin wannan waje.
Daula hotel dai tsohon gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya siyar dashi ga wani mutum, wanda aka yayyankashi har akayi gini a wannan waje.
Wakilinmu na Fadar Gwamnatin Kano, Jabir Ali Danabba ya rawaito mana, gwamnan da kansa ya jagoranci wannan aiki, sannan kuma ya nuna rashin jin dadinsa da yadda tsohuwar gwamnati ta aikata irin wannan aika aika.