Kamar yadda majalisar ɗinkin duniya ta ware yau shine ranar da aka ware na ''ƳAƘI DA SHA DA FATAUCIN MIYAGUN ƘWAYOYI TA DUNIYA'' inda shahararriyar ƙungiyar nan mai zaman kanta wadda ke rajin wayar da kan matasa kan illolin shaye-shaye wato (LESPADA) wadda ke samun jagoranci ƙarƙashin shugabancin Amb. Maryam Hassan da haɗin gwiwar NEMA, POP COLA da ita kanta hukumar NDLEA suka shirya, kuma aka ware yankin ƙaramar hukumar Nassarawa yankin Brigade Gama domin yin gajeran tattaki da wayar da kan al'umma da kuma bayyana musu illolin ta'ammali da waɗannan miyagun ƙwayoyi.
Sai dai a lokacin da kwamandan Hukumar ta NDLEA, Abubakar Idris Ahmad ya jagoranci shiga wani filin bal da ake kira da FILIN MINI suka tunkari wani bangare sai kuwa sukayi arangama da waɗannan matasa da ake zargin suna siyar da wannan ƙwayoyi da zummar gabatar da wayar da kansu da kuma gargaɗin ta'akmali da wannan miyagun ƙwayoyi ai kuwa nan take akayi arangama tsakanin Kwamandan na NDLEA da wasu daga cikin waɗannan matasa inda ya kaiwa guda cikin su cafka da hannu amma sauran matasan suka dunga kai masa sara da adda don ganin ya saki abokin su, ganin haka yasa jami'an NDLEA sukai harbi sama nan take suka zurare ta cikin wani rami dake jikin katangar filin suka gudu.
Ƴan Jarida sun tattauna da wannan kwamanda bayan da akai wannan karan batta ya kuma bayyana cewa ''Wannan ɗan ƙaramin artabu da akai tsakanin mu da waɗannan matasa yayi kama da dukan juji domin gwazarma taji tsoro duk da cewa ba kame muka fito ba domin yau ranar tattaki ce kuma munzo ne domin wayar da kan waɗannan matasa amma kuma haka ta kasance, muna tabbatarwa da al'umma jihar kano cewa zamu koma wannan guri domin tabbatar da daƙile wannan harka ta ta'ammali da miyagun ƙwayoyi, kuma muna kira ga iyayen abokan masu wannan ta'annaci dasu dena gudun waɗannan matasa, su dunga janyo su a jiki suna wa'azantar dasu kan wannan hali da suka jefa kansu maimakon korar su da ƙyamatar su''. inji shi
Amb. Maryam Hassan ta bayyana aikin shahararriyar ƙungiyar su ta LESPADA inda tace ''Gaskiya abunda muka gani yayin wannan tattaki babu daɗi kuma mu a LESPADA Bamu da aiki daya wuce taimakawa waɗanda iftila'in ta'ammali da miyagun ƙwayoyi ya afkawa sannan da janyo hankalin su wajen aikata dai-dai sabanin rashin dai-dai da kuma nuna musu manyan illolin dake yanayin da suke jefa kansu ciki, har kullum ƙofar mu a buɗe take wajen karbar masu neman agaji kan yadda za'a daƙile ko nisantar da ƴaƴan su wajen ta'ammali da miyagun ƙwayoyi ta hanyar basu ingantattun shawarwari da yimusu karatu na musamman, kuma muna kira da adena ƙyamatar masu aikatawa illa iyaka a nuna musu cewa abunda suke yi ne ba'a so kuma muddin suka bari s shirye ake a taimaka musu sannan a cigaba da mu'amala dasu kamar kowane ɗa'' inji Ambasada Maryam.