Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta fara zaman share fagen shari'a, inda ta amince da bukatar INEC na aiwatar da wasu gyare-gyare a cikin ƙunshi martanin da ta shigar a gaban kotun.
Jam'iyyar APC reshen jihar Kano ce ta shigar da ƙara gaban kotun korafe-korafen zaɓen inda take ƙalubalantar nasarar Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan Kano a zaɓen ranar 18 ga watan Maris din 2023.
Sauran mutanen da jam'iyyar APCn ta kai ƙara gaban kotun, har da hukumar zaɓe ta INEC da jam'iyyar NNPP.
A zaman kotun na yau an mayar da hankali ne, kan tsattsefe bayanai da takardun dukkan É“angarorin da ke cikin shari'ar suka shigar gaban kotun.
An É—auki lokaci ana muhawara kan kuskuren da INEC ta yi wajen rubuta sunan APC a cikin martaninsu.
Barista Yahaya Isa Abdulrashid daya daga cikin lauyoyin da ke wakiltar INEC ya kuma shaida wa BBC cewa Kotu ta riga ta amince da su gyara All Progressive Party da aka yi kuskuren rubutawa zuwa All Progressive Congress.
''Mun riga mun shigar da martaninmu, yanzu abin da ya rage shi ne a fara wannna shari'ar gadan-gadan\'', in ji shi.
Baya ga hukumar INEC da APC ta maka a gaban kotun akwai kuma Inginiya Abba Kabir Yusuf, inda ta ke kalubalantar nasarar da ya samu.
Barista Bashir Yusuf Tudun Wuzirci na cikin lauyoyin gwamna Abba Gida-Gida, ya kuma shaida wa BBC cewa sun gabatar da takardun hujjojinsu da ke nuna cewa sun yi nasara a zaɓen.
''Yanzu abin da muke jira shi ne kotun ta fara sauraron ƙorafe-ƙorafen'', in ji lauyan.
Barista Abdullahi Adamu Fagge auyan APC wadda ta shigar da ƙarar, ya ce zaman kotun na yau ,ya kawo ƙarshen gutsiri-tsoman da wasu ke yi cewa ba a shigar da ƙarar ba ma.
''Maganar gaskiya yadda aka fara zaman nan yau kamar yadda kowa ya gani kuma ya ji, zama ne da ya yi mana kyau, kuma zama ne da aka fara shi bisa nasara game da yadda al'amuran suke faruwa'', in ji shi.
Ya kuma ce ''mun tanadi duka takardun hujjojinmu da za mu gabatarwa kotun domin tabbatar da ƙorafinmu''.
Barista Ibrahim Isa Wangida na cikin tawagar lauyoyin jam’iyyar NNPP ya ce sun shirya tunkarar duk wani abu da APC za ta bijiro da shi a gaban kotun.
Ya kara da cewa ''tun farkon da kaka kawo ƙararar mun dube ta, mun kuma tunkare ta, mun kuma shigar da ƙorarrafin cewar tun farko ma bai kamata a ɓata lokaci wajen wannan shari'ar ba, saboda ita kanta kotun da aka shigar da ƙarar ma ba ta da hurumin sauraron ƙarar da wanda ya yi takara ma babu sunansa a kai''.
''Kuma akwai ƙa'idoji da dama da aka saɓa a shigar da ƙarar waɗanda idan aka yi la'akari da su ma bai kamata a ɓata lokaci a kan shari'ar ba'', in ji shi.
Jam'iyyar APC dai ta na neman kotu ta ayyanata a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamnan jihar Kano, da halastattun ƙuri'u mafi rinjaye ko kuma, idan hakan ba ta samu ba, to a ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba, tare da ba da umarnin sake zaɓe a tashoshin zaɓen da aka soke.
Kotun dai ta É—age zamanta zuwa gobe domin a saurari É“angaren masu Æ™ara da waÉ—anda ake Æ™ara, a matakin share fagen shiga shari’ar.
Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ce dai ta ayyana Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano cikin watan Maris din da ya gabata.
Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Farfesa Ahmad Doko Ibrahim ya bayyana cewa Abba Kabir ya samu ƙuri'u 1,019,602, yayin da Nasiru yusuf Gawuna na APC ya samu ƙuri'u 890,705.
BBC