A nasa ra’ayin, ɓata kudi ne kawai gwamnati ke yi wajen tafiyar da majalisun biyu.
Najeriya na da zauruka biyu na majalisar dokokin tarayya, wadda ta haɗa da Majalisar Dattaijai mai wakilai 109.
Sai kuma Majalisar Wakilan Tarayya, wadda take da wakilai 360.
A tattaunawarsa da BBC, Shekarau ya ce kamata ya yi Najeriya ta rungumi tsarin mulki irin na Birtaniya, wanda aikin ƴan majalisar bai wuce na wucin-gadi ba.
Sai dai Shekarau ya ce gyara irin tsarin na majalisar dokoki a Najeriya abu ne mai matuƙar wahala domin sai an yi gyara a kundin tsarin mulkin ƙasar.
Kuma cewarsa, akwai yiwuwar ƴan majalisar dokokin, waɗanda dole ne sai an samu amincewarsu kafin a iya sauya dokar, ba za su goyi bayan canza ta ba.
Sanata Shekarau ya ce “kowane daga cikin ƴan majalisar tarayya 469, an ba shi dama ya ɗauki ma’aikata guda biyar.”
Ya kuma ƙara da cewa “kowane kwamitin majalisar yana da ma’aikata aƙalla biyar.”
“Ko kuɗin da ake kashewa kan irin waɗannan ma’aikata abu ne da ya kamata a duba.” – In ji shi.
Shekarau ya ce ana kafa kwamitoci a majalisar dokokin ta tarayya waɗanda ba a buƙata, kuma ɓarnar kudi ne kawai da lokaci.
Majalisar Dattijan ita ce zaure mafi ƙoluluwa a batun yin dokoki a ƙasar, inda Majalisar Wakilai ke biye mata.
An dai sha tafka mahawara kan yawan kuɗin da gwamnati ke kashewa a ƙasar wajen tafiyar da gwamnati, wani abu da ake ganin za a iya yin gyara a kai, ta yadda ƙasar za ta iya amfani da kuɗin wajen samar da kayan more rayuwa ga sauran al’ummar ƙasar sama da miliyan 200.
Sai dai har yanzu babu wani yunƙuri da aka yi a hukumance wajen tabbatuwar hakan.
Ibrahim Shekarau na daga cikin ƴan majalisar dokoki na tara, sai dai ba zai kasance a majalisa ta 10 da za a ƙaddamar ba cikin watan Yuni.