Kungiyar ƙwadago ta ƙasa, NLC ta shiga yajin aiki a fadin kasa daga ranar Laraba, sakamakon karin farashin man fetur sakamakon cire tallafin mai.
Kungiyar ta NLC dai ta yi watsi da wannan abin da ta kira bita da kulli, inda ta bukaci a mayar da farashin litar mai zuwa tsohon farashi.
Da ya ke zantawa da manema labarai a karshen taron NLC na kasa a yau Juma’a, Kwamared Joe Ajaero, shugaban NLC ya ce kungiyar ta amince da yajin aikin gama-gari a fadin kasar.
“A zaman da NEC ta yi ta umurci shugabannin NLC su yi taka-tsan-tsan wajen tattaunawa da mutanen da ba su da mukami.”
“Saboda haka NLC ta yanke shawarar cewa idan har zuwa ranar Larabar mako mai zuwa, NLC, kamfanin NNPC, wanda ya sanar da tsarin farashin man fetur ba bisa ka’ida ba, ya ki amincewa da hakan, NLC da sauran kungiyoyin ta za su janye ayyukansu tare da fara zanga-zanga a fadin kasar nan har zuwa wannan lokacin.
“Hukumar NLC ta NEC ta umurci dukkan reshe ta na jihohi da kungiyoyin masana’antu da su fara shirye-shiryen shiga yajin aikin,”