Daga Barr. Abba Hikima
Abunda muka sani shine “public taking-over of private property” wato gwamnati na iya karbar gida ko filin ka ta maida shi na amfanin jama’a. Bamu san gwamnati ta dauki kayan jama’a ta mallaka wa dai-dai-kun mutane ba sai a mulkin Ganduje.
Nine lauyan yan kasuwar Holbon dake Bompai. Shaguna sama da 2,000 suka rushe wa talakawa kuma gwamnati ta siyar da rodinan jama’a na kusan Miliyan 100 a hukumance ga wani kamfani duk da Babbar Kotun Kano ta bada umarnin kada a rushe. Akan wannan har umarnin binciken MD din KSPI Dr Jibrilla, kotun Magistrate ta bada amma suka ki bi.
Nine lauyan mutanen, Kafin Agur dake Madobi, da court order da komai aka dinga baje gonakin talakawa sama Hectare 180. Aka cire musu bishiyoyin su na amfani. Aka jikkata talakawa da tsofaffi wadanda suka ki yadda da kwace musu gona. Sannan bayan an kwace aka mallaka wa yan siyasa.
Nine lauyan yan kasuwar kantin Kwari. Da court order da komai suka dinga gine tituna da hanyoyi suna gini akan magudanan ruwa suna mallakawa kan su.
Nine lauyan wani bangare na mutnen Ungogo, Gezawa da sauran su. Da court order aka dinga tuje gonakin talakawa ana mallakawa masu kudi da yan siyasa.
Nine lauyan masu gidajen kan Katsina road. Yanzu haka shekarar 2 a kotu akan hana gwamnati yin shaguna a kasan wayoyin da hayar ruwa.
Saboda haka abunda muke gani yanzu shine karbe kayan jama’a daga dai-dai-kun mutane da kuma maidawa jama’a (wato gwamnati). Wannan shine a’ala kuma abun da ya dace. Duk wani abu da ba wannan ba a bayan wannan yake. Idan akwai hakkin masu hakki sa iya bi amma ko a dokar kasa, hakkin jama’a gaba daya na gaba da hakkin dai-dai-ku.