wanda suka haddasa wannan hatsarin wata mota kawai suka gani ta wuce sai suke tunanin ko shinkafa ce nan take suka bita a ƙoƙarin su na kama motar shinkafa sun kashe kansu kuma sun yi sanadin mutuwar wasu ciki harda Ɗanbarno.
Kuma motar da suke bi ɗin bata kamu, tabbas komai da sanadi,aka ce baya tafiya a motar haya wannan karon ne yaje tasha ya hau mota ashe ajalinsa ne ya kirashi.
Marigayi Inspecta Auwalu G Danbarno
Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un
Gaskiya ne Auwalu Ɗanborno ya yi hatsari ya rasu.
Marubuci Yusuf Yahaya Gumel ya bayyana irin sanin da yaiwa Marigayi Ɗanbarno
AUWALU G ƊAN BARNO.
A 2013/2014.
Na fara saninsa sanadiyar Duniyar marubuta, ta Muhammad Lawal Barista.
Ina yawan ganin post na shi na labarai, har ma da muhawarori, ina bibiya har ta kai ina sharhi yana mayar da martani. Sannu a hankali na cigaba da bibiyarsa alaƙa na ƙarfi har ta kai mun fara magana a akwatin sirri (inbox).
Bayan na yi mafarki mun haɗu da shi a zahiri, ya yi dariya a lokacin da nake sanar masa ya kuma bayyana jin daɗinsa. Har ma ya ce ai nan da wani lokaci zai zo Gumel ma tare da Alan Waƙa.
Bayan wannan mun cigaba da mu'amala sosai ba tare da na taɓa ganinsa ba a zahiri ba. Sai bayan zuwan taron ranar marubuta na Duniya a lokacin da muka haɗu a Katsina.Mun gaisa a daddafe har ma za mu yi hoto hakan ba ta samu ba. Na kasance mai yawan bibiyar rubutunsa muna saɓawa sosai, akan wasu ababe da yawa. Amma ban taɓa mayar masa da martani mai zafi ba. Haka dabi'ata take gan cika tsaurarawa a komai ba. Kuma ina daraja shi da kallon Yaya sosai a gare shi. Saboda rasa accaunt ɗina na farko, shi ya sanya ya fita a jerin friends nawa, wanda ba mu cika magana ba.
Amma tare da hakan ko wanne post da zai yi ina bibiya. Abu daya da nake cewa idan da zan samu wani aboki da zai zamo tamkar yadda Auwalu G ɗan Barno yake da Ala ya ishe ni ji a raina na samu aboki da babu irinsa.
Tun bayan samun labarin rasuwar har zuwa yanzu da nake rubutun nan, babu wani lokaci da ya wuce ba tare da ya faɗo mini ba.
Gaskiya ne marubuta mun yi rashi, al'umma sun yi rashin mutumin kwarai.
Sunan da nake yawan kiransa da shi. shi ne AG NIGERIA.
Na saurari waƙar da Ala ya masa a baya sosai sama da adadin da zan iya bayyanawa.
Auwalu Garba ɗan Barno. ka bi a hankali yanzu, sha'anin mutum yanzu, sha'anin amana.
Bai taɓa mini laifin da na riƙe shi ba, don haka ina masa addu'ar samun rahama. Halinsa nagari ya bi shi. Allah ya yafe masa kura-kurai na shi.
A ƙarshe ina kira ga marubuta ire-iren su A AG ba su cancanta a manta da su ba har abada.
Daga Yusuf Yahaya Gumel.
Cewar marubuciya Nabila
Allahu Akbar! Allah yakai Rahama kabarinsa,ya haskaka kabari yasa Aljannace makomarsa, inama sauran maza zasui koyi da wannan kyakykyawan Hali, hakan ne yatunamin da labarin da wata kawata ta bani na facalarta da ba,afi sati uku ba walh,Yayan mijinta wato mijin facalar Nan Tata da suke zaune Gida daya,gidan na gadon kannen mazajen nasu ne da suke gidan Aure ba biya sukeba,Amma daya tashi Aure sai yaginawa Amaryar me dakuna biyar Gida yai kyau, uwar Gida sai ji tayi ankai Amarya datayi magana sai yace Mata intaga dama Nan da wata 6 ko shekara ta shirya ta koma,Kuma ba abinda yai Mata dama na Wanda zataji sanyin Auren dayai,amaryar ma ta taba Mata waya ta zageta karshe abin ma akanta ya kare na cin mutuncin dayai Mata,wacce suke zaune Gida daya wato kawar Nan tawa facalarta ita ke kwasar takaicin abinda ake Mata ita saidai tayi murmushi tace Wanda duk yayi mugunta Dan kansa.karshe dai 'yan,uwan Nan NASA ma sun hade Kai sunce yatasar musu daga gida don basuji dadin abinda yaiwa uwar gidan sa ba.😰wasu mazan basuda Adalci walh...mu ma Mata wasun mu suna da son kansu...Allah yasa ataru agyara dai.
Marubuci Hafiz Koza shima ya bada ta'aliƙi kan rubutun Marubuci mai laƙabin Aunty Baby.
TABBAS YA CIKA ADALIN NAMIJI
*(Wannan rubutun Aunty Umma Sulaiman 'Yan awaki; “Aunty Baby” ne. Ta yi shi a Facebook ranar 16 ga watan Maris, 2023. Watanni uku kenan da suka wuce).*
Wato shi Wannan Bawon Allah bazakasan ko waye shiba sai ka mu'amalance shi, da Yawa kallon da mutane suke masa ba haka Yake ba.
Sabo da Yana da son barkwanci, da yawan tsokana da faɗin gaskiya komai ɗacinta, wanda wannan Yasah baya jituwa da wasu a wannan kafar sai wayanda suka Fahimce shi.
Babbar Halayyar wannan Bawan Allah da take matukar burgeni shine kula da addini, domin Mutumina ne kwarai da gaske yana zuwa office ɗina ko gidana idan na kirawo shi akan abin daya shafi Foundation ɗina ko wani abun na daban, dalilin Haka yasah suka saba da mai gidana.
Acikin halayyar sa data burgeni shine kula da Sallah, don duk daɗin hira yana jin kiran Sallah zai tashi yaje yayi Sallah...
Mun shisshiga kasuwa dashi basau daya ba , ba sau biyu ba, Amman koda bangaren marasa sallah mukaje yana duba agogo yake dakatar da komai ya samu ruwa yayi Alwala yayi Sallah..
Ta ɓangaren Amana kuma wallahi na daɗe banga mutum mai amanarsa ba,
In Zaka bashi ajiyar kuɗi ko kadara ko ka ɗora shi akan wata sabga ta kuɗi to wallahi wallahi, in zaka shekara nawa yaddah ka waiwayi abun ka haka zaka same shi, Jama'a da Yawa sun Shaida shi mai Amana ne.
Bari na dawo kan ainihin labarin da zai tabbatar muku da cewa ya isah Adali
Kowa Yasan cewar ya kara aure kusan sati biyu da suka wuce....
Tambayar farko da nayi masa ya kayi da uwar gida batayi rigima ba ? murmushi yayi yace min Anty aini duk rigimar da zata yi bazan saurareta ba sai dai na rarrasheta .
Yace min kullum hakuri nake bata ina kwantar mata da hankali cewar ba matar da zata zo ta goge mata zane..
Sabo da tsohuwar zuma ake magani.
Yau ba'afi kwana 7 ba yazo gidana muna maganar tsadar kayan gini, sai nake ce masa ya maganar ginin ka kuwa kayi nisa, sai ya buɗe waya ya nuna min yace kinga har an gama tayel.
Nace kai kai kai gaskiya gidan nan yayi kyau , na yaba kwarai, sannan nace masa To amaryar zaka kawo nan?..
Abin da yasa nayi masa wannan tambayar sabo da nasan Yana zaune a gidan kansa , shida Uwar gidan sa , kuma gidan a wadace yake basu da takura ..
Amsar da ya bani tasani nayi shiru, kamar na saka kuka sabo da daɗi...
Yace min haba Anty ai wannan gidan na Binta ne, ita da Ƴaƴanta na ginawa, ga wadda muka sha wuya tare , Ita kadai zata tare a ciki ita da yaranta , nayi ɓangaren yara mata daban bangaren maza daban, ita kuma sama da kasa duk nata ne..
Inyaso Ita kuma Amarya in na nutsu sai nayi mata nata.
Shi kansa yasan naji daɗin maganar sa, don najinjina masa tare da yi masa godiya kamar yace ya bani kyautar gidan.
Da fatan sauran maza za suyi koyi da irin wannan Adalci na Officer
Auwal G Danbarno
Allah ya saka masa da Alkhairi ya ƙaro masa kuɗi da zaman lafiya da iyalansa..
Rahma Abdulmajid Sadiya Garba Fauziyya D. Sulaiman Binta Spikin Bilkisu Yusuf Ali Ibrahim Adam Dan Sarauta Sakina Ammani Inuwa Aīcha Yahaya Tambari Ayuba Muhammad Danzaki Haj Aisha Bala Kuki Kolo Dauda Zuwaira Kolo Aminu Kano Sa'adatu Saminu Kankia Maryam Bilyaminu Bint Zakar Hadejia Ummu Abdulmajid Hassanah Sayyada Ummy Soha Musa Asmau Ibrahim Badamasi Murja Isa Muhammad Rumasa'u Kabeer Hajara Safiyo Hamza Alqasem Isa Zahrau Ibrahim Usman Mariya M Aliyu Nabla Mimi Shafa'atu Ado Shitu Sa'adatu Baba Ahmad Zubair M Balannaji UsTazeya Ra Mu Yahanasu Shariff Kabir Amina Hassan Abdulsalam Hauwa Lawan Maiturare Aisha Adamu.
Saƙon Ta'aziyya daga Marubuci (UNCLE LARABI)👇👇
Innalillahi Wa'inna Ilaihir Raji'un! 😭 😭 😭. Na kasa bayyana irin kaduwar da nayi da Jin Rasuwar Auwal Garba Danborno.
Marubuci ne Dan'uwanmu. Wanda muka Kwashe Shekaru 23 Muna Zumunci. Tun farkon Fara Rubutuna a 2000 muke Mutunci da Zumunci.
A Shekarar 2012 ya taba taimaka min akan wasu Kayana da Suka zo daga Cotonou Wanda ake bawa ajiyar Kayan yace sai na biya wasu Himilin Kudi. Auwal Garba Danborno shi Yazo yayi mana Sulhu kasancewarsa Police Kuma a lokacin Ina Jin Yana aiki a Arear da abin ya faru na dai manta. Amma na masa waya Yazo yayi mana Sulhu.
A Shekarar 2013. Ya taba hadani da Wani lauya abokinsa suka taimakeni na Shigar da Wani Mutum da yake siyar da kayana Yana samun na abinci wato (Kayi Nayi) ya cinye min Kudi har na N1.6 Million na wancan Lokacin.
Tabbas Auwal Garba Danborno mutum ne da ba zan iya fadin kyawawan Halayensa anan ba gaba Daya. Amma mutum ne da yake son yaga ya Taimakawa na kusa dashi ko da da Shawara ne ba wai sai ya dauki kudi ya bashi ba. Wanda wannan ma kadai Ladan Sadaka ne.
Allah ya gafarta masa. Ya kyautata namu zuwan. 😭 😭.
Ya rasu akan hanyarsa ta zuwa Gonarsa Dake Ringim. Yayi Hatsarin Mota.
Ya Rasu ya bar matan Aure biyu da Yara. Mahaifinsa da Mahaifiyarsu dukkanninsu suna Raye.
Ya Rasu a yau Lahadi 25th June, 2023. Daidai da (7th Zulhijja, 1444 A. H). da Misalin 12 na Rana.
Allah ya gafarta masa. Ya kyautata namu zuwan. 😭 😭 😭. Amin summa amin.
Saƙon ta'aziyya daga marubuci Muhammad Bala Garba👇👇
Allah Ka ji ƙan Ɗanbarno
Duk wanda yasan Ɗanborno, yasan mutum ne mai kawaici da barkwanci ga kuma haƙuri. Zai yi wuya ka haɗu da shi bai sakar maka fuska ba ko da kana da tsaɓani da shi. Abu na ƙarshe da zan iya tunawa ya yi a gabana shi ne; lokacin da ake taron taya Dr. Aminu Ladan Abubakar (Alan waƙa) murnar samun sarautar Sarkin Ɗiyar Gobir a ranar Lahadi 13 ga watan Maris din 2022 (a wajen taron aka ɗauke shi hoton da yake kan profile nasa na fesbuk) a gidan rediyo Firemiyya da ke jihar Kano; bayan an bayyana zakarun gasar da aka saka an kira su an karrama su, sai aka kira shi domin ya tofa albarkacin bakinsa. Kasancewar waɗanda suka yi zarra a gasar duka mata ne, da ya zo kan daddamali ya amshi abin magana bayan ya yi godiya ga Allah ya yi salati ga Annabi (S.A.W), sai ya ce, "Naga duk waɗanda suka yi nasara a gasar mata ne, kodayake, harkar rubutu ta koma hannun mata yanzu, saboda shinkafa tayi tsada marubuta maza sun ajiye rubutu sun koma tuƙa adaidaita sahu." sai aka fashe da dariya.
Haƙiƙa Muhammad Lawan Barista ka rasa abokin muhawara a wannan kafar.
Allah Ya ji ƙan Ɗanborno, Allah Ya yafe masa, ya gafarta masa, ya albarkci bayansa, ya sa mutuwa hutu ce gare shi da sauran al'ummar Musulmai. 🙏🏽
Mohammed Bala Garba
25/6/2023