Cikin wani saƙo da mai magana da yawun tsohon shugaban Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa ta twitter ya ce, labaran da ke yawo a shafukan sada zumunta, waɗanda ke cewa Buharin ya nemi Tinubu da kada ya binciki jami'an gwamnatinsa, labarai ne na ƙanzon-kurege.
Gabanin babbar salla ne Bola Tinubu ya gana da Buhari a wata ziyara da ya kai gidansa da ke Landan lokacin wata ziyarar ta ƙashin ƙai da Tinubun ya kai Landan bayan taron harkokin kuɗi na duniya da ya halarta a birnin Paris.
To amma Mallam Garba Shehu ya ce a lokacin ziyarar Buhari da Tinubun ne kawai suka gana babu wani mutum a É—akin da suka gana, dan haka babu wanda ya san me suka tattauna.
Sanarwar ta kuma ce Buhari ya zaɓi fita daga Najeriya ne saboda gudun tsoma wa sabuwar gwamnati baki a al'amuranta.
''Da farko ya zaɓi ya zauna a gidansa da ke Daura domin samun hutu da nutsuwar da yake buƙata, to amma hakan bai samu ba, kasancewar a kullum, dare da rana, safe da yamma ɗimbin mutane ne ke ziyartarsa'', in ji Mallam Garba Shehu cikin saƙon da ya wallafa.
Ya ƙara da cewa tsohon shugaban ya tafi Landan ne domin samun hutun da yake buƙata, sannan kuma hakan zai bayar da dama ga sabuwar gwamnatin Tinubu ta gudanar da ayyukanta wajen cika alƙawuran da suka ɗaukar wa talakawan Najeriya.