Cibiyar (MiK - Infortech) da haɗin gwaiwar Makarantar koyon tsafta (School of Hygiene) sun gudanar da jarabawa ta musamma ga ɗaukacin ɗalibai Maza da mata 50 kan ilimin nazarin na'ura mai ƙwaƙwalwa wato Computer Education Yayin jawabin sa shugaban cibiyar ta (MiK - Infortech) Engr. Mahmud Isa Kawu ya bayyana dalilin su na shirya irin wannan jarabawa ga ɗalibai bayan sun samu horo na tsawon makwanni, inds yace a kullum burin su ace Matasa musamman masu tasowa sun waye da sanin na'ura mai ƙwaƙwalwa kasancewar zamanin yanzu ya zama sai da ilimin nazarin na'ura ake rayuwa kama tun daga wayoyin hannu da sauran su.
Aminu Muhammad shi ke zama sakatare na wannan cibiya ya kuma bayyana wannan yunƙuri nasu a matsayin dama da zasu samarwa matasa aikin yi a saƙaƙe musamman duba da yadda zamani ya rikiɗe ya koma sai da wannan ilimi sannan mutum zai tsira a gurare daban-daban, musamman ma'aikatun gwamnati idan mutum yana da rabon yi.
Suma kuma ɗqliban sun nuna farin cikiin su tare da godiya ga wannan cibiya da tayi ƙoƙarin damar musu da aikin yi duba ds cewa ilimi ne na musamman kuma ko ina mutum ya tsinci kansa ba zai kssance cikin duhu ba.