Gwamnatin jihar Kano ta bayyana takaicin yadda wasu ’yan fashi ke kokarin lalata kadarorin jama’a da sunan kwashe baraguzan gine-gine da gwamnatin jihar ta ruguje.
Bisa la’akari da abubuwan da suka gabata Gwamnan Jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ya umarci kwamishinan ‘yan sandan jihar da ya gaggauta kamo masu aikata irin wannan aika-aikar tare da tabbatar da cewa sun fuskanci fushin doka.
Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da gudanar da sana’o’insu, su kasance masu bin doka da oda tare da kai rahoton irin wadannan baragurbin barayin ga jami’an tsaro mafi kusa domin daukar matakin gaggawa.
Cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, yace, Gwamnan ya tabbatar wa al’ummar jihar kan jajircewar gwamnatin sa na kwato dukiyoyin al’umma da aka mallaka ba bisa ka’ida ba tare da dora jihar kan turba madaidaiciya don samun gagarumar nasara.