Hukumar Yaki da Cin hanci da rashawa ta Ƙasa, EFCC, na tuhumar tsohon gwamnan Ekiti, Dr Kayode Fayemi zargin karkatar da kudade da kuma badaƙalar naira biliyan hudu.
Wata majiya da ke kusa da hukumar ta EFCC ta ce Fayemi ya isa ofishin EFCC din ne da misalin karfe 10 na safiyar yau Alhamis, inda jami’an hukumar su ka matse shi da tambayoyi.
Majiyar tace tsohon gwamnan yana ofishin hukumar na shiyyar dake Oko Close, Off Station Road, Ilorin a Kwara domin yi masa tambayoyi kan zarge-zargen da ake masa na zamba.
A cewar majiyar, EFCC na yiwa tsohon gwamnan tambayoyi ne kan zargin badaƙalar naira biliyan 4 da kuma karkatar da kudade.
Binciken dai an ce yana da nasaba ne da yadda ake tafiyar da kudade a lokacin da ya ke gwamnan Ekiti.
Fayemi ya kasance gwamnan jihar daga 2018 zuwa 2022 kuma ya mika wa Gwamna Biodun Oyebanji a watan Yunin 2022.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, a wata wasika mai dauke da kwanan watan 12 ga watan Mayu, ta gayyaci tsohon gwamnan da ya bayyana a ofishinta na jihar Kwara a ranar 18 ga watan Mayu bisa zargin da ake masa na karkatar da kudaden jama’a.